Dalilin Takaddamar Siyasa A Jihar Filato
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Dalilin Takaddamar Siyasa A Jihar Filato
Jun 16, 2023
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Matakin sallamar shugabannin kananan hukumomi 17 da gwamna Caleb Muftwang ya dauka a jihar Filato bisa umarnin majalisar dokokin jihar ya haifar da rikicin da dole sai da hukumar 'yan sanda ta shiga tsakani.

Shin dokar kasar Najeriya ce ta yarje wa gwamnan har ya iya daukar wannan mataki?
Idan babu dokar da ta ba shi hurumin yin hakan, ke nan siyasa ce?

Ku saurari shirin Najeriya a yau ku ji amsoshin da masana  suka  bayar game da dacewa ko rashin dacewar korar shugabannin kananan hukumomin jihar Filato 17 da gwamna Caleb Muftwang ya yi.