Yadda Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya Ya Shafi Makwabtanta
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Yadda Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya Ya Shafi Makwabtanta
Jun 19, 2023
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya furta cewa wasu kasashen dake makwaftaka da Najeriya suna jin radadin cire tallafin man da aka yi fiye ma da ‘yan kasar Najeriya. 

Shirin namu na yau ya tsallaka kan iyaka ya shiga wasu kasashe makwaftan Najeriya domin mu ji ko abin da shugaban majalisar dattawan ya fada da gaske ne ko kuwa.

Shin ko cire tallafin mai a Najeriya ya shafi kasar Nijar?

Shirin ya tuntubi wani basarake a Accra, kasar Ghana, wanda ya bamu labarin mai a kasar.