Dalilan Gwamnatin Jihar Kano Na Dakatar Da Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Dalilan Gwamnatin Jihar Kano Na Dakatar Da Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu
Jan 25, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Gwamnatin Kano  ta dakatar da daukacin makarantun kudi na Jihar da nufin sake nazari a kan yadda ake gudanar da su, a cewarta.

Matakin dai ya biyo bayan kururuwar da al’umma ta yi bayan gano gawar Hanifa Abubakar, wata daliba da ake zargin shugaban makarantar da take ya sace, ya kuma kashe ta.

A shirin Najeriya a Yau za mu ji hikimar yin hakan da ma yadda hakan zai shafi ilimi a Jihar.